Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen Yaki Sun Makara Wajen Fuskantar Barazana Ga Fadar White House - 2002-06-21


Jami'an Amurka sun ce jiragen saman yakin da aka tura domin tare wani dan karamin jirgin da ya keta haddin sararin samaniyar da aka hana shiga a kewayen fadar White House ranar laraba da maraice, sun makara kafin su kai ga jirgin.

Jami'an, wadanda suka ce kada a bayanna sunayensu, sun ce jiragen yakin sun tashi cikin lokacin da aka kayyade musu na mayar da martani, amma kuma ba su kai sama inda zasu iya yin wani abu ba har sai mintoci hudu a bayan da dan karamin jirgin kirar Cessna mai inji daya ya fice daga yankin samaniyar da aka haramta shiga.

Daga baya, jiragen yakin sun kai ga wannan jirgi, suka yi masa rakiya zuwa birnin Richmond mai tazarar kilomita 160 a kudu da nan washington, inda aka yi wa matukin jirgin tambayoyi.

Jami'an suka ce wannan lamari ya nuna irin wuyar da ake fuskanta wajen kare kai daga hare-hare ta sama.

Hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya, ta ce matukin yayi kuskuren shiga cikin wannan yankin ne a lokacin da yake kokarin kaucewa hadari, kuma a bisa dukkan alamu ba za a tuhume shi da aikata wani laifi ba.

An kwashe ma'aikata da sauran mutanen dake cikin fadar ta White House na wani dan lokaci, amma kuma shugaba Bush ya ci gaba da zama a ciki.

XS
SM
MD
LG