Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ravalomanana Ya Ki Yarda Da Kudurin Kungiyar OAU - 2002-06-23


Magoya bayan Marc Ravalomanana, daya daga cikin mutane biyun dake ikirarin shugabancin kasar Madagascar, sun yi watsi da kiran da kungiyar Hada kan Kasashen Afirka ta OAU tayi na a gudanar da sabon zabe a kasar.

Mukarraban Mr. Ravalomanana sun bayyana sanarwar da kungiyar OAU ta bayar a zaman maras tasiri, suna masu zargin shugabannin kungiyar da laifin goyon bayan abokin adawarsa Didier Ratsiraka.

A wajen taron da suka yi a kasar Ethiopia, shugabannin OAU sun ce ba su amince da kowane daya daga cikin mutanen biyu a zaman shugaban Madagascar ba, suka kuma ce ba za a yarda wani ya hau kan kujerar Madagascar a tarurrukan OAU ba har sai an kafa gwamnati ta halal a kasar.

Mr. Ratsiraka, tsohon shugaban da ya jima yana mulkin kasar, wanda kuma ya halarci taron na birnin Addis Ababa, ya amince da wannan kuduri na kungiyar OAU. Ita ma kasar Faransa, wadda tayi wa Madagascar mulkin mallaka, ta ce tana goyon bayan kudurin na kungiyar OAU.

XS
SM
MD
LG