Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Ruwan Afirka Ta Kudu Zai Isa Kuryar Kudancin Duniya Domin Ceto Mutane 100 - 2002-06-24


Nan bada jimawa ba wani jirgin ruwan ayyukan agaji na Afirka ta Kudu zai kai ga gefen daskararriyar kankarar da ta kewaye, ta rutsa da wani jirgin ruwan kasar Jamus mai dauke da mutane fiye da 100 a nahiyar Antarctica dake kuryar kudancin duniya.

Jami'ai sun ce gobe talata da asubahi jirgin ruwan na Afirka ta Kudu mai suna "Agulhas" zai kai ga yankin, watau kwana guda tun ma kafin ranar da aka tsammaci isarsa.

Sai dai kuma duk da haka, sai jirgin ya tsaga ya ratsa ta cikin daskararriyar kankara mai fadin daruruwan kilomita kafin ya kai ga inda jirgin ruwan na kasar Jamus ya kafe.

Jirgin ruwan Afirka ta Kudun ya bar birnin Cape Town mako guda da ya shige, domin ya ceto masana kimiyya na kasar Rasha su 79, da ma'aikata 28 na jirgin ruwan Jamus, a bayan da jirgin nasu ya kafe cikin kankara kwanaki 13 da suka shige, bayan da ya yi jigilar kayayyakin bukatu zuwa ga wani sansanin bincike na Rasha dake doron wannan hamadar kankara.

XS
SM
MD
LG