Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Kasashe Masu Arzikin Masana'antu Zai Gabatar Da Shiri Kan Afirka A Yau Alhamis - 2002-06-27


A yau alhamis idan Allah Ya nuna mana, taron kolin kasashe takwas masu arzikin masana'antu da ake yi a Kananaskis a kasar Canada, zai gabatar da wani shirin tallafawa Afirka, wanda aka tsara da nufin bunkasa cinikayya da zuba jari a wannan nahiyar dake can kuryar baya cikin masu cin moriyar hada-hadar tattalin arzikin duniya.

Wakilin Muryar Amurka a can Calgary, Barry Wood, ya ce shugabannin kasashen Afirka hudu, Olusegun Obasanjo na Nijeriya da Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu da Abdel-Aziz Bouteflika na Aljeriya da kuma Abdoulaye Wade na Senegal, tare da babban sakataren MDD dan kasar Ghana, suna halartar taron kolin na bana. Shugabannin suna gabatar da cikakken bayani ne game da shirinsu na NEPAD, watau Sabon Shirin Kawancen Raya Kasashen Afirka.

Frank Chikane, limamin kirista ne, kuma mai bada shawara ga shugaba Thabo Mbeki na Afirka ta Kudu. Ya ce shirin NEPAD, ba na tattalin arziki ne kawai ba. Ya ce shiri ne na kare hakkin Bil Adama, kuma kuduri na dawwamar da zaman lafiya a wannan nahiya da ta tagayyara. Mr. Chikane ya kuma ce NEPAD akida ce ta tabbatar da dimokuradiyya tare da yin mulki cikin gaskiya da adalci.

ACT: CHIKANE: "African leaders have seized the opportunity of this historical moment to deal with the......"

FASSARA: Shugabannin kasashen Afirka sun rungumi wannan dama ta musamman da ake da ita a yanzu ta fuskantar irin matsalolin dake addabar nahiyar. Zan iya cewa sun tari aradu da ka ne, a saboda irin tsananin matsalolin da muke fuskanta. Sun kuma dauki alkawari, suka kudurta cewa tilas ne a kawo karshen yake-yake na babu gaira babu dalili da ake fama da su a nahiyar Afirka. Wannan ba karamin kuduri ba ne. END ACT

TEXT: Mr. Chikane ya ce shirin NEPAD shiri ne da babu kamarsa, domin kuwa shiri ne kacokam na nahiyar Afirka, wanda shugabannin nahiyar suka zauna suka tsara a zaman yadda suke hangen raya nahiyar. Wiseman Nkuhlu, shi ma dan Afirka ta Kudu ne, kuma shine babban jami'i a sakatariyar NEPAD. Ya ce tun farkon fari, shirin NEPAD, kundin alkawari ne a tsakanin shugabannin Afirka da jama'arsu.

ACT: NKUHLU: "At the start, the program may not appear to be that radical, but the centerpiece is around one,..."

FASSARA: Da farko dai, za a ga kamar wannan ba sabon shiri ne kacokam ba, to amma kuma idan an duba sosai za a ga cewa ya dogara ne a kan akida kwaya daya tak: watau dangantaka a tsakanin shugabannin Afirka da al'ummar kasashensu. NEPAD shiri ne na batutuwan mulki wadanda ya zamo tilas shugabanninmu su lura da su. Da farko, shugabanni su fahimci cewa jama'a sun ba su amana ne, kuma dukkan hakkin jama'a yana kansu, sannan kuma su fahimci cewa akwai hakkin 'yan'uwansu shugabanni a kansu. END ACT

TEXT: Mr. Nkuhlu ya ce a wannan lokaci da ake renon shirin na NEPAD, watakila kasashen Afirka biyar zuwa goma ne kawai zasu iya rungumar akidarta ta yin mulki tsakani da Allah. A bisa dukkan alamu, kasashe masu arzikin masana'antu dake halartar wannan taron koli zasu duba su ga ko wadanne kasashe ne zasu iya rungumar wannan akida tsakani da Allah, domin su zamo wadanda za a fi bai wa agaji, da zuba jari da kuma kulla cinikayya. Kasashen masu arzikin masana'antu sun ce sun kuduri aniyar bunkasa harkokin bada agajin tattalin arziki ga kasashen Afirka. Mr. Chikane ya ce shirin NEPAD yana takalar batun akidar mayar da duniya falle guda a fannin tattalin arziki, domin Afirka ma tana son taka rawa sosai a wannan tsarin tattalin arziki da ya dogara kan cinikayya.

ACT: CHIKANE: "If we don’t do anything about it, Africa is likely to be marginalized even further and....."

FASSARA: Idan har ba mu yi wani abu a kan (shiga cikin tsarin tattalin arzikin duniyar ba), to za a ci gaba da kara mayar da Afirka saniyar ware. Yana da matukar muhimmanci mu tsoma hannu domin canja lamarin. END ACT

TEXT: Mr. Nkuhlu, wanda ke shugabantar kwamitin tsare-tsare na NEPAD, ya bayyana a fili cewar yana yin adawa da wasu matakan sauye-sauyen da masu bada rance irinsu bankin duniya da asusun IMF suke bukatar lallai sai an dauka. Musamman ma, ya bayyana adawa sosai da yin riga malam zuwa Masallaci ta hanyar rage kudin fito na kayayyakin da kasashen Afirka ke saye daga kasashen waje.

ACT: NKUHLU: “No country ever started off by opening and liberalizing and allowing all kinds of imports....”

FASSARA: Babu wata kasar da take fara kulla huldar cinikayya, ko makamancin haka, ta hanyar kyalewa a shigar da komai cikin kasarta, abinda ke janyo mummunan hadari ga batun samar da abinci ga al'ummarta. Kasashen Afirka ne kawai ake ingiza su domin suyi wannan. Mun kuma fahimci cewa yin hakan yana yin barazana ga kokarin samar da wadataccen abinci ba tare da tsangwama ba ga al'ummarmu, a saboda yadda ake tsara wadannan manufofi, da kuma ganin cewa ba 'yan Afirka din ne suke gudanar da shirin ba. Tilas sai su 'yan Afirka sun kasa kunne domin yin abubuwan da masu bada kudaden ke fadi. END ACT

TEXT: Mr. Nkuhlu ya ce cikin 'yan shekarun nan Afirka ta yi hasarar 'yancinta, a saboda dogarar da tayi kan agajin kasashen waje. Wannan ba shine karon farko da sunan Afirka ke fitowa kan gaba a taron kolin tattalin arziki ba. An gabatar da shirye-shiryen soke basussukan da ake bin kasashen Afirka a tarurrukan kolin kasashe masu arzikin masana’antu a 1998 da 1999. Amma kuma firayim minista Jean Chretien na Canada ya maida batun Afirka ya zamo babban batu a wannan taron kolin. Kuma shaidar wannan ita ce kasancewar shugabannin Afirka guda hudu a wurin wannan taro na Canada.

XS
SM
MD
LG