Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbe Wani Fada Aka Kashe Shi A Kasar Colombia - 2002-06-29


'Yan bindiga a kasar Colombia, sun bindige suka kashe wani fada na kiristoci mabiya darikar Roman Katolika, malamin addini na baya-bayan nan da aka kashe a yakin basasar kasar dake kara yin muni.

Hukumomi sun ce an kashe Jose Hilario Arango ranar alhamis da daddare a Cali, birnin da aka kashe babban fada Archbishop Isaias Duarte ciki a watan Maris.

Dukkan mutanen suna masu sukar lamirin 'yan tawayen Colombia masu ra'ayin gurguzu.

Jami'ai suka ce 'yan sanda sun kashe mutum guda a inda aka kashe fada Arango, amma ba a fahimci ko mutumin yana da hannu wajen kashe fadan ba.

A halin da ake ciki dai, shugaba Andres Pastrana na Colombia, ya bada sanarwar tukuicin dala miliyan biyu ga duk wanda ya tsegunta musu labarin da zai kai ga kama manyan shugabannin 'yan tawaye.

XS
SM
MD
LG