Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Mika Jajen Amurka Game Da Kashe Mataimakin Shugaban Kasar Afghanistan - 2002-07-07


Shugaba Bush yayi tur da kashe mataimakin shugaban kasar Afghanistan, Haji Abdul Qadir, da aka yi asabar, ya kuma mika tayin Amurka na taimakawa wajen farauto wadanda suka aikata kisan.

Mr. Bush ya ce Abdul Qadir mutumin kwarai ne wanda ke kwadayin ganin 'yanci da kwanciyar hankali sun wanzu a kasarsa da yake kauna. Mr. Bush ya ce wannan kisa ya karawa Amurka karfin guiwa a kudurinta na ganin ta wanzar ad zaman lafiya a Afghanistan.

Wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wanene ba, sun yi ta barin wuta a kan motar da ta dauko Malam Abdul Qadir a kusa da ofishinsa a Kabul, babban birnin kasar. An kuma kashe direbansa a wannan harin. Shaidu sun ce maharan sun yi shiga kamar masu gadi ne. An kama masu gadi da dama a ofishin mataimakin shugaban, a saboda sun ki su dauki wani matakin hana wannan harin.

Kasashe da dama su ma sun yi tur da wannan kisa. Kamfanin dillancin labaran Xinhua na gwamnatin China ya ce ma'aikatar harkokin wajen kasar ta bayyana girgizarta da wannan lamarin, ta kuma aike da sakon ta'aziyya ga al'umma da kuma gwamnatin Afghanistan.

Ita ma ma'aikatar harkokin wajen Iran, ta ce wannan hari aiki ne na mutanen da ba su son ganin an samu kwanciyar hankali a Afghanistan.

XS
SM
MD
LG