Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Farko Da Aka Zaba Bayan Yakin Basasa Zata Fara Zama A Saliyo - 2002-07-12


A yau jumma'a shugaba Ahmed Tejan Kabbah na Saliyo zai bude zaman majalisar dokokin farko da aka zaba a bayan yakin basasar shekaru goma.

Kaddamar da majalisar dokokin, zata biyo bayan zaben da aka yi acikin watan Mayu, inda shugaba Kabbah ya samu gagarumar nasarar kara wa'adin shekaru biyar kan karagar mulki.

A lokacin jawabinsa na kama mulki a wannan sabon wa'adin ranar 19 ga watan Mayu, Mr. Kabbah yayi kira ga dukkan 'yan Saliyo da su hada kai a bayansa domin yakar yunwa da zarmiya.

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta "Human Rights Watch" ta kuma ce tilas ne sabuwar gwamnatin kasar ta tabbatar da cewa an hukumta wadanda suka aikata laifuffukan yaki.

Cikin rahoton da ta bayar jiya alhamis, kungiyar mai hedkwata a birnin New York ta ce har yanzu ba a magance muhimman dalilan da suka janyo yakin basasar kasar ta Saliyo ba, watau zarmiya da cin hanci da suka yi kanta, da kuma rashin kwarin mulki bisa aiki da doka.

XS
SM
MD
LG