Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Spain Da Maroko Suna Shirin Kai Ruwa Rana - 2002-07-13


Spain ta tura jiragen ruwan yaki da sojoji domin su kare tsibiran da take ikirarin cewa nata ne a kusa da Maroko, bayan da aka ga sojojin Maroko suna kafa sansanin bincike a wani dan karamin tsibiri da suke gardama a kai.

Jami'an gwamnatin Spain sun bayyana matakin da Maroko ta dauka da cewa "na nuna rashin abota ne."

A ranar alhamis, Maroko ta tura sojoji kwaya 12 zuwa wani tsibiri da babu wani mutum a kansa wanda Spain take kira Perejil, domin gudanar da aikin da ta kira sha gaban bakin haure da 'yan ta'adda.

Maroko ta ki yarda da bukatar da Spain tayi cewar lallai ta janye daga kan wannan tsibiri, wanda dutse ne kawai da babu komai kansa, wanda kuma tazarar mita 200 kacal yake da ita daga bakin gabar kasar Maroko.

A can birnin Brussels, Kungiyar Tarayyar Turai, wadda Spain memba ce a cikinta, tayi tur da matakin da Maroko ta dauka a zaman keta haddin diyaucin Spain, amma kuma tayi kira ga kasashen biyu da su zauna su warware rikicin.

Wannan lamari shine rikicin diflomasiyya na baya-bayan nan a tsakanin kasashen biyu, tun lokacin da Maroko ta janye jakadanta daga birnin Madrid haka kwatsam a cikin watan oktoba.

XS
SM
MD
LG