Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Kabbah Ya Bude Zaman Majalisar Dokoki - 2002-07-13


A jiya Jumma'a shugaba Ahmed Tejan Kabbah ya bude zaman majalisar dokoki na farko tun bayan yakin basasar shekaru goma a kasar Saliyo, inda ya bayyana cewa a yanzu kam, dimokuradiyya ta zauna da gindinta a kasar.

A lokacin da yake magana a birnin Freetown, shugaba Kabbah ya ce zaman lafiyar da al'ummar Saliyo suke cin moriya suke kuam bukin karramawa, ya samu ne a sanadin kawancen kasashen duniya.

Ya ce "abokanmu ba su taba yin watsi da mu ba," yana mai yabawa da ayyukan kiyaye azaman lafiyar da Majalisar Dinkin Duniya take gudanarwa a kasarsa.

Shugabannin Afirka hudu sun halarci bukin na jiya Jumma'a -- Olusegun Obasanjo na Nijeriya, John Kuffour na Ghana, Lansana Conte na kasar Guinea da kuma yahya Jammeh na Gambiya.

Shugaba Kabbah ya ce yana shirin maida hankali wajen kyautata rayuwar talakawan kasar Saliyo.

XS
SM
MD
LG