Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'in Kula Da Shawagin Jirage A Sama Na Switzerland Yayi Na'am Da Rawar Da Ya Taka Wajen Karawar Jirage... - 2002-07-14


Jami'in kula da shawagin jirage a sararin samaniya na Switzerland wanda ke bakin aiki a lokacin da jirage biyu suka yi karo a sama cikin watan nan, ya ce na'urori da tsarin kula da zirga-zirgar jiragen sama suna da nasu laifi a wannan hadarin.

Wannan jami'in da ba a bayyana sunansa ba, ya fada ta cikin wata sanarwar da lauyansa ya bayar jiya asabar cewa mutane, da injuna masu kwakwalwa, da dokokin aiki, da na'urorin hango jirage da na aikewa da sakonni duk sun taka rawa a wannan karo da jiragen biyu suka yi.

Ya ce aikinsa ne ya hana abkuwar irin wannan hadarin. Ya mika jajensa ga iyalan mutane 71 da suka mutu a hadarin.

Mutane fiye ad dubu daya suka taru jiya asabar a yankin gabashin kasar Rasha a wajen du'a'in tunawa da mutane 28 daga cikin wadanda suka mutu.

A ranar 1 ga watan nan na Yuli, wani jirgin saman fasinjan Rasha da wani jirgin safarar kayayyaki sun kara a can sama a yankin bakin iyakar kasashen Switzerland da Jamus da kuma Austriya.

XS
SM
MD
LG