Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan bindiga Sun Kashe Mutane Akalla 24 A Bangaren Indiya Na Yankin Kashmir - 2002-07-14


'Yan sanda a bangaren Indiya na yankin Kashmir sun ce suna zaton Musulmi 'yan aware ne suka kashe mutane akalla 24 a wata unguwar share-ka-zauna dake kusa da Jammu, babban birnin jihar na lokacin hunturu, jiya asabar da maraice.

Shaidu sun ce 'yan bindigar da suka yi shiga kamar malam addinin Hindu, sun kutsa cikin yankin Qasim Nagar suka jefa gurneti da dama kafin su bude wuta da bindigogi.

Mutane akalla 30 sun ji rauni a wannan harin, yayin da jami'ai suke fadin cewa akwai alamun yawan wadanda suka mutu zai karu.

Babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan harin. Amma wani babban jami'in 'yan sanda ya ce hukumomin Indiya suna kyautata zaton wannan aiki ne na kungiyar Lashkar-e-Toiba, mai hedkwata a kasar Pakistan, wadda kuma take gwagwarmayar kwato yankin daga karkashin ikon Indiya.

XS
SM
MD
LG