Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mai Shari'a Ta Ki Yarda Da Amsa Laifin Da Moussaoui Yayi - 2002-07-19


Wata mai shari'a a kotun tarayya ta ki yarda da amsa laifi na ba-zata da Zacarias Moussaoui yayi jiya alhamis gabanta. Moussaoui shine mutum guda daya tak da aka tuhuma a kotu dangane da hare-haren ta'addanci na ranar 11 ga watan Satumba.

Mai Shari'a Leonie Brinkema ta nace a kan lallai Moussaoui ya ce ya zauna na tsawon mako yana tunanin wannan abu, inda ta nuna alamun cewar tana ganin kamar ya rude.

Haka kwatsam Mr. Moussaoui ya mike cikin kotu ya ce yana son amsa laifin zargin da ake yi masa, har ma ya ce ya san wanda ya kai hare-haren 11 ga watan Satumba.

Moussaoui ya yayi rantsuwar yin biyayya ga Osama bin Laden, watau yayi masa mubayi'a, sannan kuma shi dan kungiyar ta'addanci ta al-Qa'ida ne.

Mai shari'ar ta ja kunnen Moussaoui kan cewa yana fa yarda da cewar ya aikata laifuffukan da lauyoyin gwamnati suke zarginsa da aikatawa ke nan.

XS
SM
MD
LG