Ma'aikatan majalisun birane da na kananan hukumomi a Afirka ta Kudu zasu gana da hukumominsu a yau Jumma'a, kuma ana kyautata zaton zasu sanya hannu kan yarjejeniyar kawo karshen yajin aikin da suka yi makonni biyu da rabi suna yi.
A ranar laraba wakilan kungiyoyin ma'aikatan da na hukumomin da suka dauke su aiki suka cimma yarjejeniya kan karin albashi, suka kuma tura ga membobinsu domin neman amincewarsu.
Hukumomi sun ce a shirye suke su rattaba hannu a kan yarjejeniyar idan sassan biyu sun gana yau Jumma'a.
Wannan yarjejeniya zata yi karin kashi 8 daga cikin 100 ga ma'aikatan da albashinsu ya wuce dala 315 a wata, yayin da ma'aikatan da albashinsu bai kai haka ba zasu samu karin kashi 9 daga cikin 100.
Wannan yajin aiki ya kawo cikas ga ayyukan kwashe shara da sauran ayyuka tun ranar 2 ga watan yuli a manyan biranen Afirka ta Kudu.