Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wuta Ta Kama A Tankin Ajiye Mai Na ChevronTexaco A Nijeriya - 2002-07-21


Wata wuta mai karfin gaske ta kama da ci a wani tankin ajiye man fetur na kamfanin ChevronTexaco, a dandalin jigilar mai zuwa kasashen waje na Escravos asabar din nan a yankin kudu maso gabashin Nijeriya.

An ce tsawa ce ta tayar da wannan gobara a dandalin man da kwanakin baya wasu mata suka mamaye na tsawon kwanaki goma, suka gurgunta ayyukan mai.

Ba a samu wani rahoto na jin rauni ba.

Ya zuwa asabar din nan kuma, wasu mata dake da bukatu kamar na makon jiya, suna ci gaba da mamaye wasu tasoshin famfon man fetur na kamfanin. Wadannan tasoshin sune suke tura mai zuwa dandalin Escravos, daga inda ake lodinsa zuwa kasashen waje.

Jami'an kamfanin ChevronTexaco sun ce suna shirin ganawa da matan a cikin mako mai zuwa domin kokarin kawo karshen wannan mamaya.

XS
SM
MD
LG