Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kori James Traficant Daga Cikin Majalisar Wakilan Amurka - 2002-07-25


Majalisar wakilan tarayya ta Amurka ta jefa kuri'a kusan ba tare da hamayya ba, domin korar James Traficant, dan jam'iyyar Democrat daga Jihar Ohio, saboda ya keta dokokin da'a na majalisar.

An jefa wannan kuri'a cikin daren laraba, inda 'yan majalisa su 420 suka goyi bayan korarsa, dan majalisa kwaya daya tak ya jefa kuri'ar rashin yarda.

Wannan shine karo na biyu kawai tun shekarar 1865 da majalisar ta kori wani wakilinta.

A cikin watan Afrilu, wata kotun Ohio ta samu Traficant da laifin karbar cin hanci, kaucewa biyan haraji, da kuma yin zamba, ciki har da tilastawa ma'aikatan ofishinsa suna yi masa aiki a gona da gida da kuma cikin karamin jirgin ruwansa. A mako mai zuwa za a yanke masa hukumci, kuma yana iya fuskantar daurin shekaru fiye da bakwai a gidan kurkuku.

Kafin a jefa kuri'ar, Traficant ya shaidawa zauren majalisar inda kowa yayi tsit yana zaune zugum, cewar bai aikata laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa ba, amma kuma ya ce a shirye yake ya tafi kurkuku ya kuma yi hasarar komai.

Ya dora laifin wannan fitina tasa a kan wata makarkashiyar da ya ce gwamnati ta kulla masa.

Sauran 'yan majalisar suka ce babu wani abin dadada zuciya a korar dan'uwansu dan majalisa, amma kuma shaidar laifin Traficant tana da yawa.

Traficant, wanda sau tara ana zabensa daga Jihar Ohio, yayi suna a saboda irin sutura ta dabam, da aski na dabam, da kuma jawabai na dabam da yake gabatarwa a zauren majalisa.

Haka kuma, yayi kaurin suna wajen furta kalmomi na batsa tare da zagin abokan aikinsa.

XS
SM
MD
LG