Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Saliyo Da MDD Sun Bayyana Sunayen Alkalai 8 Na Kotun Shari'ar Laifuffukan Yaki - 2002-07-26


MDD da gwamnatin Saliyo sun bayyana sunayen alakalai guda takwas wadanda zasu yi shari'ar mutanen da aka tuhuma da aikata laifuffukan yaki a lokacin yakin basasar da aka yi a wannan kasa dake Afirka ta Yamma.

Kakakin MDD, Fred Eckhard, ya ce kafin karshen wannan watan alkalan zasu hau kan kujerunsu a wannan kotun bin kadin laifuffukan yaki ta musamman.

Mr. Eckhard ya ce gwamnatin kasar Saliyo da kuma babban sakataren MDD, Kofi Annan, sune suka zabi wadannan alkalai.

Kakakin na MDD ya ce alkalai daga kasashen Canada da Kamaru da kuma Saliyo zasu yi aiki cikin ainihin kotun da zata bi kadin laifuffukan na yaki, sannan kuma lakalai daga kasashen Nijeriya, da Gambiya da Saliyo da Britaniya da kuma Austriya zasu yi aiki a kotun daukaka kara.

Har ila yau an bayyana sunayen wasu alkalai biyu daga Zambiya da Ghana a zaman na wucin gadi.

A lokacin yakin basasar shekaru 10 da aka yi a Saliyo, 'yan tawayen kungiyar "RUF" sun yi kaurin suna a saboda tsananin mugunta da rashin imanin da suka nuna, ta hanyar kashewa da yin fyade wa dubban fararen hula, tare da yanke gabobin wasu dubban mutanen.

XS
SM
MD
LG