Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Sudan Da Madugun 'Yan Tawaye Sun Amince Da Shirin Zaman Lafiya - 2002-07-28


Shugaban Omar Hassan al-Bashir na Sudan da madugun 'yan tawaye John Garang, sun gana a karon farko, inda suka amince da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma makon jiya da nufin kawo karshen yakin basasar shekaru 19 a kasar.

Mutanen biyu sun gana na tsawon sa'o'i biyu jiya asabar a Kampala, babban birnin Uganda. Shugaba Yoweri Museveni na Uganda shine ya jagoranci wannan ganawa da suka yi.

A cikin sanarwar hadin guiwar da suka bayar, shugabannin na Sudan sun yi alkawarin warware sauran batutuwan da suka rage a zagaye na gaba na shawarwarin neman zaman lafiyar da za a yi a cikin wata mai zuwa.

Dukkan bangarorin sun ce tattaunawar ta gaba, zata maida hankali kan raba ikon mulki ta hanayr shigar da 'yan tawaye cikin gwamnati, da hanyoyin rarraba arzikin mai na kasar da kare hakkin bil Adama da kuma tsagaita wuta.

Haka kuma, sun yaba da gagarumar yarjejeniyar da aka cimma a makon da ya shige game da batutuwa guda biyu mafiya muhimmanci a yakin basasar da aka jima ana yi a kasar Sudan, watau ba da jama'a ikon cin gashin kai, tare da cire batun addini a harkar mulki.

XS
SM
MD
LG