Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iraqi Ta Alakanta Tattaunawa Kan Binciken Makamai Da Sake Nazarin Takunkumin Da Aka Sanya Mata - 2002-08-06


Ministan harkokin wajen Iraqi, Malam Naji Sabri, ya ce tilas gayyatar da kasarsa tayi na tattaunawa kan sake kyale sufetocin makamai su shiga kasar, ta tafi kafada da kafada da batun kokarin dage takunkumin da aka sanya wa kasarsa.

Malam Sabri ya shaidawa 'yan jarida a kasar Jordan cewar Iraqi ta rungumi kudurorin MDD wadanda suka bukaci warware batun na Iraqi baki daya.

Babban sakataren MDD, Kofi Annan, ya ce zai nemi gwamnatin Iraqi da ta fayyace ko gayyatar da tayi wa babban sufeton makamai, Hans Blix, kan ya ziyarci Bagadaza tana nufin cewa da gaske ne ita Iraqin tana son a koma ga ayyukan binciken makamai.

A halin da ake ciki dai, Amurka tayi watsi da gayyatar da Iraqi tayi wa 'yan majalisar dokokin Amurka kan su gudanar da na su binciken a cikin Iraqi, tana mai bayyana wannan a zaman kokarin neman sukunin watayawa a bangaren Iraqin.

XS
SM
MD
LG