Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kotun Zimbabwe Ta Goyi Bayan Turawa Manoma - 2002-08-08


Babbar kotun Zimbabwe ta yanke hukumcin da ya bada karin lokacin numfasawa ga turawa manoma, wadanda aka bai wa wa'adin tsakar dare domin ficewa daga gonakinsu.

Kotun ta yanke hukumci a jiya laraba cewa babu dama gwamnati ta kwace gonakin turawan dake karkashin jingina, har sai ta sanar da bankuna ko kamfanonin da suka karbi jinginar wadannan gonaki.

Wannan hukumci yana iya shafar daruruwa daga cikin turawa manoma su kusan dubu 3 a kasar ta Zimbabwe, wadanda tilas su fice daga cikin gonakinsu, ko kuma a kai su kotu karkashin dokar sake rarraba filaye ta kasar.

Shugaba Robert Mugabe ya ajiye wa'adin korar manoman daga gonakinsu a cikin watan Mayu. Ya ce an dauki wannan matakin ne domin gyara danniyar da aka yi karkashin mulkin mallakar turawan Ingila, inda aka dauki kashi 70 cikin 100 na gonakin da suka fi kyau a kasar aka damka su hannun turawa wadanda kwata-kwata yawansu kashi 1 ne tal a cikin 100 na al'ummar kasar.

XS
SM
MD
LG