Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Fara Sanya Idanu kan Bakin Dake Shigowa Daga Wasu Kasashe - 2002-08-13


Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta zabi ranar 11 ga watan Satumba, watau ranar cikar shekara guda da harin ta'addancin da aka kawowa Amurka, ta zamo ranar da zata fara aiki da wani sabon tsarin sanya idanu kan baki 'yan kasashen waje dake ziyara a nan Amurka.

Za a fara da yin gwajin wannan tsari na tsawon kwanaki 20 a filayen jiragen sama da tasoshin jiragen ruwa, da bakin iyakoki da dama, kafin a aiwatar da shi baki daya a dukkan wuraren da baki kan shigo Amurka.

Wannan tsari zai tanadi daukar hoton yatsun baki daga kasashen Iran, da Iraqi, da Libya, da Sudan da kuma Syria, kasashe biyar da Amurka ta ce suna cikin masu goyon bayan ayyukan ta'addanci.

Za a dauki hoton yatsun dalibai da baki daga wasu kasashen dabam, idan har hukumomi suka yi imanin cewa suna iya yin barazana. Daga nan za a gwada hoton yatsun nasu da hotunan yatsun mutanen da aka san cewa 'yan ta'adda ne ko masu aikata laifuffuka.

Masu kare hakkin Larabawa da Musulmi a nan Amurka sun ce wadannan sabbin ka'idoji na nuna tsanar wani jinsi ne.

XS
SM
MD
LG