Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Tana Adawa Da Hukumcin Da Kotun Shari'ar Musulunci Ta Yanke - 2002-08-23


Gwamnatin Nijeriya ta ce tana yin adawa sosai da hukumcin da wata kotun shari'ar Musulunci ta yanke cewar a jefe wata matar da aka samu da laifin yin zina.

Cikin wata sanarwar da ya bayar alhamis, ministan shari'a na Nijeriya, Kanu Agabi, ya ce lauyoyin gwamnati zasu taimakawa lauyoyin Amina Lawal a kokarin ganin cewa wata kotun ta daukaka kara ta soke wannan hukumci.

A ranar litinin wata kotun shari'ar Musulunci a Jihar Katsina dake arewacin Nijeriya ta ki yarda da daukaka karar da Amina Lawal tayi dangane da yanke mata hukumcin kisa. A watan Maris aka fara samun Amina da laifi, aka kuma yanke mata hukumcin na kisa.

Wannan hukumci ya janyo suka daga kasashen duniya dabam-dabam. Gwamnatocin kasashen waje da kungiyoyin kare hakkin bil Adama sun bukaci gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo da ta tsoma baki ta hana aiwatar da wannan hukumci.

A karkashin shari'ar Musulunci, ana iya yanke hukumcin kisa kan mutumin da ya taba yin aure ko yana da aure aka kuma same shi da laifin zina.

XS
SM
MD
LG