Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babbar Kotu A Zimbabwe Ta Bai Wa Manoma 54 Sukunin Kara Numfasawa - 2002-08-28


Wata babbar kotu a kasar Zimbabwe, ta soke takardun iznin korar wasu turawa manoma su 54, wadanda aka yi niyyar kwace gonakinsu karkashin shirin gwamnati na sake rarraba filayen noma.

Alkalin kotun, Benjamin Paradza, ya soki lamirin gwamnati, yana mai cewa ta ki ta yi aiki da dokokin da ta kafa da kanta kan hanyoyin da za a bi wajen karbar gonakin turawa.

Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, ya umurci turawa manoma su dubu 2 da 900 da su mika gonakinsu ga bakakaen marasa galihu, amma kuma ba za a biya su diyya ba.

An kama manoma su akalla 200 wadanda suka ki bin umurnin da aka ba su na ficewa daga gonakin nasu a ranar 8 ga watan Agusta.

Mr. Mugabe ya ce an tsara wannan manufa ce domin gyara irin tabargazar da aka aikata lokacin mulkin mallakar turawan Ingila, a lokacin da aka bada kashi 70 cikin 100 na gonakin da suka fi kyau a kasar ga turawa wadanda yawansu bai wuce kashi 1 cikin 100 na al'ummar kasar ba.

XS
SM
MD
LG