Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Pakistan Sun Hana Benazir Bhutto Yin Takara - 2002-08-30


Jami'an zabe a kasar Pakistan sun ki yarda da yunkurin tsohuwar firayim minista, Benazir Bhutto, na yin takara a babban zaben da za a yi cikin watan Oktoba.

Jami'ai suka ce sun ki yarda da takardun neman tsayar da ita yin takarar kujera a majalisar dokoki ta kasa, saboda sau biyu kotu tana samunta da aikata laifi tun daga lokacin da sojoji suka kwace mulki kusan shekaru uku da suka shige.

Tsohuwar firayim ministar tana zaman gudun hijira na radin kanta lokacinda aka yi mata shari'ar a bayan idanunta.

Malama Bhutto tayi komawa gida domin yin takara a zaben tare da yakar tuhume-tuhumen da har yanzu ake yi mata.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Pakistan, Janar Pervez Musharraf, ya ce za a kama Malama Bhutto da wani hambararren firayim ministan, Nawaz Sharif, idan har suka kuskura suka taka kasar domin wannan zabe na ranar 10 ga watan Oktoba.

XS
SM
MD
LG