Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sudan Ta Dakatar Da Tattauna Zaman Lafiya Da 'Yan Tawaye - 2002-09-02


Gwamnatin Sudan ta dakatar da tattauna zaman lafiya da 'yan tawayen kudancin kasar, a bayan da suka kame wani gari mai muhimmanci a karshen makon nan da ya shige.

Ministan harkokin wajen Sudan, Mustafa Osman Isma'il ya fada a yau litinin cewa an dakatar da tattaunawa a saboda abinda ya kira "Yanayin da ya wakana a sanadin farmakin sojan da 'yan tawaye suka kai," da kuma kama garin Torit.

A jiya lahadi 'yan tawayen kungiyar SPLA suka kama wannan garin, amma gwamnati ta ce ta tura sojojinta domin su sake kwato shi daga hannun 'yan tawayen.

Wani kakakin 'yan tawayen ya shaidawa Muryar Amurka cewa bai kamata kama garin na Torit da suka yi ya shafi shirin samar da zaman lafiya ba. Ya ce ai 'yan tawayen ba su janye daga shawarwarin neman zaman lafiya ba a lokacin da gwamnati ta kwace garin Gogrial na kudancin kasar.

XS
SM
MD
LG