Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Bush Ya Gana Da Shugabannin Majalisar Dokoki Kan batun Iraqi - 2002-09-04


Jami'an gwamnatin Amurka sun ce shugaba Bush zai yi alkawarin neman goyon bayan majalisar dokoki kafin ya dauki matakan soja a kan Iraqi.

Shugaban ya gana da shugabannin majalisar dokoki daga dukkan jam'iyyu biyu inda suka tattauna batun Iraqi.

Shugaba Bush ya ce kwadayin da shugaba Saddam Hussein yake yi na kerawa da mallakar makaman kare dangi, yana barazana sosai ga Amurka da duniya baki daya.

'Yan majalisar dokoki da yawa, cikinsu har da shugaban masu rinjaye a majalisar dattijai, Tom Daschle, sun yi kira ga shugaban da ya bayyana muhimman dalilan daukar matakan soja a kan Iraqi.

Mr. Daschle ya ce majalisar dokoki tana son ta san dalilin da ya sa "fadar shugaban ta kuduri aniya, a yanzu, cewar zata ci gaba da wannan yunkuri, koda kuwa babu wata kasar da ta goyi bayanta."

Nan gaba a yau laraba sakataren tsaro Donald Rumsfeld zai gudanar da taro cikin sirri da dukkan 'yan majalisar dattijai, domin yi musu bayani.

A jiya talata, Mr. Rumsfeld ya ce nan bada jimawa ba gwamnatin shugaba Bush zata gabatar da bayani na sirri da zai goyi bayan ikirarinta na cewa Saddam Hussein yana dab da kera makaman nukiliya.

XS
SM
MD
LG