Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Suna Mayar Da Martani Game Da Tayin Iraqi - 2002-09-17


Britaniya da Faransa sun bayyana taka tsantsan da shawarar Iraqi ta kyale sufetocin makaman MDD su koma cikin kasar, yayin da Rasha da China suka yi lale marhabin da wannan.

Wata mai magana da yawun firayim minista Tony Blair na Britaniya, ta ce gwamnatin shugaba Saddam Hussein ta jima tana yaudarar duniya game da batun binciken makaman.

Ministan harkokin wajen Faransa, Dominique de Villepin, ya ce a yanzu, tilas ne a tabbatar da cewa shugaba Saddam Hussein ya cika alkawuran da ya dauka.

Ministan harkokin wajen Rasha, Igor Ivanov, ya shaidawa 'yan jarida a New York cewa an kawar da barazanar yaki a Iraqi ta hanyar kokari tare da hadin kan kasashen duniya. Ya ce babban aikin dake gaba a yanzu shine tabbatar da cewa sufetocin sun koma bakin aikinsu ba tare da jinkiri ba. Ya ce babu wata bukatar wani sabon kudurin Kwamitin Sulhun MDD kafin sufetocin su koma bakin aikinsu.

Ministan harkokin wajen China, Tang Jiaxuan, ya ce gwamnatinsa zata ci gaba da yin aiki da kasashen duniya wajen samo hanyoyin siyasa na warware batun Iraqi karkashin inuwar MDD.

XS
SM
MD
LG