Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ta Amsa Cewar Ta Sace 'Yan Kasar Japan A Shekarun Baya - 2002-09-17


A karon farko, Koriya ta Arewa ta furta cewa ta sace 'yan kasar Japan a cikin shekarun 1970 da 1980.

Shugaba Kim Jong Il na Koriya ta Arewa ya nemi gafarar sace mutanen yau talata a lokacin wata ganawa mai tarihi da yayi da firayim minista Junichiro Koizumi na Japan a birnin Pyongyang.

Mr. Kim ya ce jami'an leken asirin Koriya ta Arewa sun sace 'yan kasar Japan su 11, suka yi amfani da su wajen koyon harshe da al'adun 'yan Japan.

A can baya, Koriya ta Arewa ta musanta sace kowa.

Mr. Kim ya ce ba za a sake sace wani ba, ya kuma ce an hukumta wadanda suka aikata wancan na baya.

Furta wannan da yayi ta kawar da sauran shingen da ya rage na kulla dangantakar jakadanci a tsakanin Japan da Koriya ta Arewa.

XS
SM
MD
LG