Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Goce da Harbe-Harbe A Kasar Ivory Coast - 2002-09-19


An goce da musanyar wuta yau alhamis da asubahi a Abidjan, babban birnin kasar Ivory Coast, ko Cote D'Ivoire.

Shaidu sun ce an fara harbe-harbe da kananan bindigogi, daga baya kuma aka goce da harbe-harben bindigogi masu zazzage harsashi tsakanin karfe 3 da karfe 4 na asubahi har ya zuwa safiya agogon kasar. Har ila yau an bada rahoton yin harbe-harbe a garin Bouake.

Kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya ambaci ministan tsaron Ivory Coast, Moise Lida Kouassi, yana fadin cewa an kashe mutane biyar, cikinsu har da kwamandan yankin Bouake a tsakiyar kasar, Leftana-kanar Dagrou Loula.

Har yanzu babu wani haske kan wannan lamari. Amma wasu kafofin labarai sun ambaci jami'ai suna fadin cewa wasu sojojin da suka kufula ne suke bayyana rashin jin dadinsu da shirin da ake yi na sallamar daruruwan sojoji daga aiki.

Wannan fitina ta barke a daidai lokacin da shugaban kasar, Laurent Gbagbo, yake rangadi a nahiyar Turai. A cikinwata sanarwar da aka bayar daga birnin Rum, mukarrabansa sun ce ana kwantar da wutar wannan fitinar.

Kasar Ivory Coast ta fada cikin rikicin siyasa a shekarar 1999, a lokacin da sojoji suka hambarar da gwamnatin shugaba Henri Konan Bedie. An samu tashin hankali a lokacin zabubbukan 2000 a bayan da aka hana shugaban hamayya, Alassane Ouattara, tsayawa takara a zabe.

XS
SM
MD
LG