Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawaye Suna Damarar Fuskantar Hari Daga Sojojin Gwamnatin Ivory Coast - 2002-09-27


Mazauna birnin Bouake dake hannun 'yan tawaye a kasar Ivory Coast suna zaman jiran farmakin da sojojin gwamnati zasu kai.

Mazauna birnin sun buya cikin gidajensu a yau Jumma'a, a bayan gargadin da gwamnati tayi cewar nan bada jimawa ba sojoji masu biyayya ga gwamnati zasu kai farmaki a kan cibiyoyin 'yan tawaye.

'Yan kasashen waje su akalla dubu daya sun fice daga birnin tare da rakiyar sojojin Faransa.

Har ila yau sojoji masu tawayen suna rike da garin Korhogo wanda shi ma ke arewacin kasar.

Mutane akalla 400, akasarinsu 'yan tawaye, sun mutu a sanadin wannan bore na sojoji da aka fara yi a makon da ya shige a wasu wurare uku na kasar. Ba tare da jinkiri ba, sojojin gwamnati sun sake kwace birnin Abidjan. Daga cikin wadanda aka kashe har da ministan harkokin cikin gida da wani tsohon shugaban soja na kasar.

A birnin Abidjan, an gudanar da tarurrukan gangamin nuna goyon bayan gwamnati. A yankunan da 'yan tawayen suka kama kuma, mazauna sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga 'yan tawayen, suna zargin gwamnati da zarmiya tare da nuna wariya ga Musulmin arewacin kasar. Wasu sojoji masu bore sun ce suna tawaye ne domin nuna rashin yarda da shirin sallamarsu daga aikin soja.

Nijeriya ta tura jiragen saman yaki guda uku domin taimakawa gwamnatin Ivory Coast wajen yakar 'yan tawayen.

Membobin Kungiyar Kasuwar Tattalin Arzikin Afirka ta Yamma, ECOWAS, suna shirin gudanar da taron koli ranar lahadi domin tattauna rikicin na Ivory Coast.

XS
SM
MD
LG