Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Cilla Makami Mai Linzami, Amma Bai Samu Wanda Aka Yi Niyya Ba - 2002-09-27


Isra'ila ta ce ba ta yi nasarar samun mutumin da ta auna ba a lokacin da jirginta mai saukar ungulu ya kai hari a wani yankin dake shake da mutane a birnin Gaza, amma kuma makamai masu linzamin da ta harba sun raunata mutane da dama, cikinsu har da yara 15.

Da farko, Isra'ila ta ce ta kashe wannan babban jami'in kungiyar 'yan kishin Falasdinu ta Hamas, Mohammed Deif, to amma kuma hamas ta ce wannan rahoto na Isra'ila karya ne.

An kashe dogarawa biyu cikin motar Mohammed Deif, sannan aka raunata wasu fararen hular dake kusa da wurin da motar take a daidai lokacin.

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Kofi Annan, ya bukaci Isra'ila da ta daina kai hare-hare kan yankunan da suke shake da jama'a.

XS
SM
MD
LG