Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Ivory Coast Sun Lashi Takobin Kai Nasu Farmakin - 2002-10-08


'Yan tawaye a kasar Ivory Coast sun lashi takobin kaddamar da farmaki na ramuwar gayya, a bayan da suka fatattaki sojoji masu biyayya ga gwamnati da suka kai musu hari a birni na biyu wajen girma a kasar.

Sojojin gwamnati dake kokarin kwace Bouake daga hannun 'yan tawayen, sun kutsa har tsakiyar birnin jiya litinin suna harba kwanson nakiya tare da yin luguden wuta da manyan bindigogi. Amma kuma majiyoyin soja sun ce a bayan da aka gwabza kazamin fada, sojojin na gwamnati sun ja da baya suka koma bayan gari.

Mazauna birnin Bouake sun ce sun ji kararrakin harbe-harbe yau talata da safe, a yayin da ake samun rahotannin da suka sabawa juna kan ko wane bangare ne ke rike da Bouake.

Gwamnati ta kai farmaki a bayan da ta ki yarda da shirin tsagaita wutar da jami'an diflomasiyyar Afirka ta Yamma suka gabatar.

Shugabannin 'yan tawaye suka ce sun fatattaki sojojin gwamnatin ne daga Bouake, kuma a yanzu zasu bi sawunsu da wani harin nasu na kansu.

Bouake, wanda ke yankin tsakiyar Ivory Coast, da wasu biranen arewacin kasar, sun fada hannun 'yan tawaye tun lokacin da suka kaddamar da bore a ranar 19 ga watan Satumba.

A jiya litinin, sojojin 'yan tawaye sun kama garin Vavoua na yammacin kasar, wanda ke kusa da gonakin noman Cocoa na kasar.

XS
SM
MD
LG