Ghana da Uganda sun yarda, domin radin kansu, su kyale sauran kasashen Afirka da su auna kamun ludayin tsare-tsarensu na tattalin arziki da siyasa.
An bada wannan sanarwa a wurin taron kwanaki biyu na Sabon Kawancen Raya Nahiyar Afirka, NEPAD, a birnin Johannesburg a kasar Afirka ta Kudu.
Wannan taro na jami'ai daga kasashe 60, ya mayar da hankali ne a kan batun auna kamun ludayin juna, daya daga cikin muhimman matakan shirin NEPAD na habaka bunkasar tattalin arziki da wanzar da mulki nagari a nahiyar.
Shugabannin Afirka, wadanda ke neman hanyoyin bunkasa nahiyar ta hanyar samo jarurruka daga kasashen waje, sune suka kafa wannan shiri na NEPAD.