Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutumin Da Aka Harba Dazu Da Safe Ya Mutu A Asibiti - 2002-10-22


'Yan sanda suna binciken wani harbin da aka yi dazu da safe a wani gari mai makwabtaka da nan birnin Washington a cikin Jihar Maryland. Har yanzu dai hukumomi ba su alakanta wannan harbin da harbe-harben da wani shu'umi dan kwanton bauna yayi makonni yana yi a wannan yanki ba, amma kuma ana tafiyar da binciken tamkar harbin shu'umin ne.

An yi wannan harbi da sanyin safiyar yau talata daidai lokacin da jama'a ke gaggawar zuwa wuraren ayyukansu a cikin karamar hukumar Montgomery, inda wannan shu'umin da ya addabi mutane ya fara kashe mutane biyar.

'Yan sanda suka ce mutumin da aka harba direban wata motar safa ce dan shekara 40 da haihuwa. An harbe shi a kirji a lokacin da yake tsaye a kan matakalar shiga cikin motar. An dauke shi cikin jirgin sama mai saukar ungulu zuwa wani asibiti a garin Bethesda dake kusa da nan. Labarin dake zuwa da dumi-duminsa, ya ce cikin 'yan mintocin da suka shige wannan direba ya mutu.

'Yan sanda sun mayar da martani ta hanyar toshe dukkan hanyoyin motar dake kewaye da wurin, kamar yadda suke yi a baya a duk lokacin da shu'umin ya kai hari.

Wannan harbi ya zo a daidai lokacin da 'yan sanda ke kokarin shawo kan wani mutumin da ake kyautata zaton maharbin ne da ya sake tuntubarsu ta waya kamar yadda yayi kokarin yi.

Baturen 'yan sanda a karamar hukumar Montgomery, Charles Moose, ya ce wani mutumin da masu bincike ke sha'awar yi wa magana sosai ya kira su, amma ba su fahimci abinda yake fada ba.

Moose ya bukaci mutumin da ya sake kiransu, ta yadda a cewarsa zasu fahimci abubuwan da yake fada. Bai yi karin haske ba.

Wannan shu'umi ya kashe mutane 9 ya raunata wasu guda 3 tun daga ranar 2 ga watan Oktoba. Yadda yake auna mutane haka siddan yana dirka musu harsashi babu zato babu tsammani, ya haddasa fargaba da zullumi a zukatan mutanen dake zaune a nan ciki da kuma wajen birnin Washington. Yau makonni biyu ke nan makarantu a wannan yanki ba su kyale yara su fita waje su yi wasa, yayin da aka soke dukkan wasannin motsa jiki da ake yi a waje.

XS
SM
MD
LG