Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Tamil Tigers Na Sri Lanka Sun Ce A Yanzu Kam A Shirye Suke Su Shiga Cikin Harkokin Siyasar Kasar - 2002-11-03


'Yan tawayen Tamil Tigers na kasar Sri Lanka sun ce suna son shiga cikin harkokin siyasar kasar, a bayan da suka yi kusan shekaru 19 suna yakar hukumomi a birnin Colombo domin ganin an ba su kasarsu 'yantacciya.

A karshen shawarwarin neman zaman lafiyar kwanaki hudu yau lahadi a kusa da birnin Bangkok, babban jami'in shawarwari na 'yan tawayen, Anton Balasingham, ya shaidawa 'yan jarida cewar a shirye 'yan tawayen Tamil Tigers suke su amince da kasancewar wasu kungiyoyin siyasar dabam a yankunan dake hannunsu, kuma suna son shiga cikin siyasar dimokuradiyya a Sri Lanka.

Wannan sauyin ra'ayi na ba-zata ya zo a karshen zagaye na biyu na tattaunawar neman zaman lafiyar da kasar Norway ke shiryawa tsakanin sassan na Sri Lanka, wadda kuma ake gudanarwa a kasar Thailand. A lokacin da 'yan tawayen Tamil Tigers da gwamnati suka gana a karon farko cikin shekaru 7 a watan Satumba, 'yan tawayen sun ce zasu iya amincewa da "ikon cin gashin kai mai kauri" a yankunan da 'yan kabilar Tamil suke da rinjaye, suka kuma yi watsi da bukatarsu ta neman 'yantacciyar kasa daga Sri Lanka inda 'yan kabilar Sinhala suke da rinjaye.

Tun ma kafin wannan sanarwa ta yau, jami'an gwamnati da na 'yan tawayen Sri lanka duk sun ce ana samun ci gaba fiye da yadda ake zato a wajen tattaunawar. A jiya asabar, babban jami'in shawarwarin gwamnati, G.L. Peiris, ya ce sassan biyu sun samu gagarumin ci gaba. Shi ma Mr. Balasingham ya bayyana kwarin guiwa.

Jami'ai sun yi kashedin cewa har yanzu da sauran aiki a gaba, amma kuma sanarwar hadin guiwar da suka bayar ta ce "dukkan bangarorin sun nuna halayya masu nagarta na karfafa guiwa, da sasantawa" a wajen tattaunawar tasu.

Mutane dubu sittin da biyar sun mutu, yayin da wasu dubban daruruwa suka rasa matsuguni a yakin basasar na kasar Sri Lanka. Har ila yau, wannan yaki na kusan shekaru 20 ya nakkasa tattalin arzikin wannan tsibiri.

XS
SM
MD
LG