Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka 20 Suna Tattauna Shirin NEPAD A Abuja - 2002-11-03


Shugabannin kasashe 20 a nahiyar Afirka suna ganawa yau lahadi a Abuja, babban birnin Nijeriya, domin tattauna yadda za a aiwatar da shirin NEPAD.

Manufar wannan shiri na NEPAD ita ce shawo kan kasashe masu arziki da su zuba jari a kasashen Afirka, su kuma yafe musu basussuka, yayin da su kasashen na Afirka zasu bada tabbacin cewar zasu yi mulki na kwarai.

Jami'an Nijeriya sun ce ya kamata kasashen Afirka su ringa auna kamun ludayin 'yan'uwansu domin tabbatar da cewa suna aiki da muhimman dokokin dimokuradiyya da na kare hakkin bil Adama. Sai dai kuma a cikin makon da ya shige, Afirka ta Kudu ta bayyana dari-dari da wannan shiri na auna kamun ludayin juna a tsakanin kasashen Afirka.

Wani jami'in Turai dake ziyara a Afirka ta Kudu, ya fada a ranar Jumma'a cewa kawar da tabbacin yin mulki na kwarai, yana iya sanya shugabannin kasashe masu arziki na duniya su dawo daga rakiyar wannan shiri na NEPAD.

XS
SM
MD
LG