Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijeriya Zata Gudanar Da Zabubbuka A Watannin Maris Da Afrilu Na Shekara Ta 2003 - 2002-11-06


Jami'an Nijeriya sun ce kasar zata gudanar zabubbukan shugaban kasa da saura a tsakanin watan Maris da Afrilu na shekara mai zuwa.

Za a gudanar da zabubbukan a ranaku dabam-dabam har tsawon wata guda daga ranar 29 ga watan Maris zuwa 29 ga watan Afrilu.

Wannan sanarwa ta zo a daidai lokacin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC, take shirya gudanar da zaben kananan hukumomi, wanda sau biyu ana jinkirtawa saboda matsaloli na rajistar masu jefa kuri'a.

A yanzu, ana zaton gudanar da zaben na kananan hukumomi a watan Disamba.

Nijeriya ta kaddamar da gagarumin aiki na yin rajistar masu jefa kuri'a domin zaben na shugaban kasa. Wannan zaben shugaba shine zai zamo na farko tun lokacin da aka zabi shugaba Olusegun Obasanjo a shekarar 1999.

Shugaba Obasanjo ya ce zai sake yin takarar wannan kujera.

XS
SM
MD
LG