Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Gangamin Kawar Da Cutar Shan Inna A Afirka Ta Yamma - 2002-11-10


A cikin makon nan kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka kaddamar da wani sabon gangamin allurar rigakafin kamuwa da cutar shan inna a yankin Afirka ta Yamma, inda suke fatan kare yara miliyan 60 daga wannan cuta.

Hukumar Lafiya ta Duniya, ita ce ke jagorancin wannan gagarumin gangami tare da Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF.

Hukumar lafiya ta duniya, wadda ke fatan kawar da cutar shan inna a duniya nan da shekara ta 2005, ta ce an dakile yaduwar wannan cuta sosai idan an kwatanta da 'yan shekarun baya, amma kuma har yanzu ana fama da ita sosai a kasashe kamar Nijeriya da Nijar.

Wani wakilin Muryar Amurka a birnin Geneva, hedkwatar hukumar lafiyar ta duniya, ya ce a cikin wannan shekarar, an samu rahotannin mutane 136 da suka kamu da wannan cuta a Nijeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a doron nahiyar Afirka.

Daga can Jamhuriyar Nijar kuwa, abokiyar aikinmu Halima Djimrao ta ce har yanzu akwai iyayen dake daukar cewa akwai wata manufa, boyayyiya, game da wannan aikin allurar rigakafi. Halima ta tattauna da mataimakin shugaban Hukumar Kula da Ayyukan Rigakafi a Nijar, Malam Magaji Jadi, wanda ya bayyana irin matsalolin da suke fuskanta wajen gudanar da wannan aikin.

XS
SM
MD
LG