Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Waje Powell Yayi Tur Da Shugabannin Kiristoci Masu Sukar Lamirin Musulmi Da Musulunci - 2002-11-14


Sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, yayi tur da kalamun da shugabannin kiristoci masu rikau suke yi na sukar Musulmi da Musulunci, yana mai cewa tilas ne a yi watsi da irin wannan kiyayya da suke nunawa Musulmi.

A lokacin da yake magana yau alhamis da shugabannin 'yan kasuwa a ma'aikatar harkokin waje, Mr. Powell ya ce irin surutan da wadannan mutane keyi an sukar lamirin Musulmi na munana martabar Amurka, kuma ba za a bar irin wannan ya ci gaba ba.

Wannan furuci na Mr. powell ya zo kwana guda a bayan da shi ma shugaba Bush ya soki lamirin wadannan kalamun batunci, yana mai fadin cewa ba su yi kama da ra'ayoyin gwamnatinsa ko kuma na akasarin Amurkawa ba.

A cikin kalamun da suka yi a watan da ya shige, shugaban wata kungiyar kiristoci 'yan ra'ayin rikau da ake kira Christian Coalition, Pat Robertson, ya ce Musulmi sun fi 'yan Nazi muni, yayin da shi kuma Reverend Jerry Falwell ya ce Annabi Muhammad (s.a.w) dan ta'adda ne. Daga baya dai, Mr. Falwell ya nemi gafara.

XS
SM
MD
LG