Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Tawayen Ivory Coast Sun Ki Yarda Da Tayin Gudanar Da Kuri'ar Raba-Gardama - 2002-11-20


'Yan tawayen Ivory Coast sun ce ba zasu nazarci tayin shugaba Laurent Gbagbo na gudanar da kuri'ar raba-gardama a kasar ba, suna masu fadin cewa ya bayyana wannan ne kawai a gaban wasu, bai gabatar musu da shi a rubuce ba.

Jami'in shawarwari na 'yan tawaye, Sidiki Konake, ya shaidawa Muryar Amurka yau laraba cewa watakila Mr. Gbagbo yayi wannan tayi kan kuri'ar raba-gardamar ce kawai domin ya lallashi 'yan kasuwa na Ivory Coast.

Mr. Gbagbo ya bayyana wannan tayin nasa ne ranar talata lokacin da yake ganawa da shugabannin 'yan kasuwa a birnin Abidjan.

'Yan tawaye suna son a yi gyara ga tsarin mulkin kasar, wanda suka ce yana nuna kyamar 'yan tsirarun arewaci da Musulmin kasar. Har ila yau sun bukaci shugaba Gbagbo da yayi murabus, a kuma gudanar da sabbin zabubbuka.

'Yan tawaye sun kaddamar da bore ranar 19 ga watan Satumba, kuma cikin dan kankanin lokaci suka kwace yankunan arewacin kasar.

An yi wata guda ana aiki da shirin tsagaita wuta.

XS
SM
MD
LG