Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Red Cross Ta Ce Mutane Fiye Da 200 Suka Mutu A Nijeriya - 2002-11-24


Shugaban kungiyar agaji ta Red Cross a Nijeriya ya ce mutane fiye da 200 aka kashe a kwanaki hudun da aka shafe ana tabka rikicin addini.

Emmanuel Ijewere yayi kiyasin cewa wasu mutanen su dubu 11 sun rasa gidajensu, yayin da wasu daruruwa suka ji rauni a fadan da aka yi ta gwabzawa a garin Kaduna dake arewacin kasar. Ya ce wannan adadi na yawan mutanen da suka mutu da kungiyar ta Red Cross ta bayar, ya kunshi gawarwakin da aka kirga a kan tituna da kuma dakin ajiye gawarwaki na asibitoci ne, bai hada da gawarwakin mutanen da 'yan'uwansu suka binne ba.

Wannan fada ya barke a ranar laraba. Jami'ai suka ce wata zanga-zangar da aka yi kan sharhin da wata jarida ta buga game da zaben sarauniyar kyau ta duniya, ta rikide ta koma fada a tsakanin Musulmi da Kirista a Kaduna.

Masu shirya zaben sarauniyar kyaun sun dage wannan gasa suka mayar da ita zuwa London a kasar Ingila. A yau lahadi da safe wani jirgin saman da aka yi haya dauke da 'yan mata fiye da 80 masu yin takara a gasar ya sauka a filin jirgin saman Gatwick na London, a bayan da ya taso cikin dare daga Abuja, babban birnin Nijeriya.

Har ila yau, masu shirya zaben sarauniyar kyau ta duniyar sun ce sun yi fatan wannan gasa ta su, wadda suka ce babu abinda ya kamo kafarta a cikin abubuwan da jama'a ke kallo a telebijin, zata hasakaka tare da bunkasa harkokin yawon shakatawa da bude idanu a Nijeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka.

A maimakon haka, wannan gasar ta harzuka 'yan Nijeriya dake ikirarin cewa tana karfafa fasikanci.

XS
SM
MD
LG