Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Gasar Sarauniyar Kyau Ta Duniya Sun Isa London daga Nijeriya... - 2002-11-24


Shugaban kungiyar agaji ta Red Cross a Nijeriya, Emmanuel Ijewere, ya ce mutane fiye da 200 aka kashe a kwanaki hudun da aka shafe ana tabka rikicin addini a garin Kaduna dake arewacin kasar.

An ci gaba da tashin hankali cikin daren jiya asabar, duk da cewa an girka sojoji da 'yan sandan kwantar da tarzoma masu yawa cikin garin na Kaduna.

Shugaban kungiyar Red Cross a Nijeriya, Emmanuel Ijewere yayi kiyasin cewa wasu mutanen su fiye da dubu 10 sun rasa gidajensu, yayin da mutane dubu daya suka ji rauni a fadan da aka yi ta gwabzawa a tsakanin Musulmi da Kirista. Har ila yau an lalata Masallatai da majami'u.

Wannan tashin hankali ya barke a sanadin sharhin da wata jarida mai suna "This Day" ta buga inda ta ce da zamanin Annabi Muhammad (saw) ne a yanzu, to kuwa da ya amince da zaben sarauniyar kyau ta duniya, kuma watakila ma da ya zabi matar aure daga cikin masu takarar.

Jaridar ta "This Day" ta fada a yau lahadi cewar ta kori 'yar jaridar da ta rubuta wannan sharhi (Isioma Daniel); sharhin da akasarin Musulmi suka dauka a zaman na batunci.

Masu shirya zaben sarauniyar kyaun sun dage wannan gasa suka mayar da ita zuwa London a kasar Ingila. A yau lahadi da safe wani jirgin saman da aka yi haya dauke da 'yan mata fiye da 80 masu yin takara a gasar ya sauka a filin jirgin saman Gatwick na London, a bayan da ya taso cikin dare daga Abuja, babban birnin Nijeriya.

Har ila yau, masu shirya zaben sarauniyar kyau ta duniyar sun ce sun yi fatan wannan gasa ta su, wadda suka ce babu abinda ya kamo kafarta a cikin abubuwan da jama'a ke kallo a telebijin, zata hasakaka tare da bunkasa harkokin yawon shakatawa da bude idanu a Nijeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka. A maimakon haka, wannan gasar ta harzuka 'yan Nijeriya dake ikirarin cewa tana karfafa fasikanci.

Nijeriya ta samu damar karbar bakuncin zaben sarauniyar kyau ta duniyar ce a bayan da 'yar Nijeriya mai suna Agbani Darego ta zamo sarauniyar kyau ta duniya a shekarar da ta shige.

XS
SM
MD
LG