Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daya Daga Cikin Manyan Kungiyoyin 'Yan Tawayen Burundi Ta Ki Yarda Da Yarjejeniya - 2002-12-02


Daya daga cikin manyan kungiyoyin 'yan tawayen kasar Burundi, ta ki yarda ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati, tana mai cewa an yi sauyi ga abubuwan dake rubuce cikin yarjejeniyar.

Tun fari, wani kakakin kungiyar 'yan tawaye ta F.D.D. ya ce a yau litinin kungiyarsa zata rattaba hannu kan yarjejeniyar a wurin taron kolin dake samun halartar shugabannin Afirka da dama, wadanda ke kokarin kawo karshen yakin basasar Burundi.

Amma kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce kungiyar ta ki yarda da wani kalami cikin yarjejeniyar wanda ke cewa tuni an warware sauran batutuwan siyasa a cikin yarjejeniyar Arusha ta 2000. Kungiyar 'yan tawayen ta ce kalamin da ta yarda a yi amfani da shi ya fayyace cewar ana ci gaba da tattaunawa kan batutuwan siyasar.

Shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya dage bukin sanya hannu kan yarjejeniyar, ya bukaci wakilan sassan biyu da su koma ga yin shawarwari.

Mutane fiye da dubu 200 aka ce sun mutu a yakin basasar da aka yis hekaru 9 ana yi a kasar Burundi tsakanin 'yan tawaye 'yan kabilar Hutu da rundunar sojojin kasar wadda 'yan kabilar Tutsi suka kanainaye.

XS
SM
MD
LG