Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Sallar Azumi Na Shugaba Bush Ga Dukkan Musulmin Duniya - 2002-12-05


Ina mai farin cikin aikewa da gaisuwa tare da sakon fatar alheri ga dukkan wadanda ke bukukuwan Sallar Azumi, Eid el-Fitr, Sallar da ta kawo karshen watan Ramadan mai tsarki ga dukkan Musulmi.

A cikin watan Ramadan Allah Ya fara sauko da KalmominSa ga Annabi Muhammad a cikin Qur'ani. Musulmi suna yawaita karantawa da karrama Qur'ani a cikin wannan wata. A cikin wata gudan da ya shige, Musulmi sun kauracewa abinci da abin sha daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana, domin sake mayar da hankali tare da karfafa imaninsu, da kuma yawaita sadaka da karimci.

Musulmi a fadin duniya sun nuna jinkai suka kuma taimakawa mutanen dake cikin matukar bukata. A kan ajiye abinci a titunan birane da garuruwa domin talakawa da marasa galihu su samu abin buda-baki. Haka kuma, a kan rarraba sadakar abinci da riguna da kudi domin tabbatar da cewa kowa da kowa ya samu wani abu daga cikin abubuwan da Allah Ya huwace wa bil Adama. A lokuta da dama, Musulmi sukan gayyaci mabiya addinai dabam domin su yi buda-baki tare, matakin da ya nuna irin karimci da zaman tare da kuma hakuri da mabiya wasu addinai.

A lokacin Sallar Azumi, Musulmi suna bukin kawo karshen azumi tare da irin falalar da suka samu daga karfafa ibada. Yadda ake gudanar da bukuwan Sallar Azumi sun sha bambam a kasashe dabam-dabam, daga kunna fitilu a Misra, zuwa ga wasan wuta a Pakistan, zuwa ga gayyatar tsoffi wajen cin abinci a Nijar. A fadin duniya, 'yan'uwa da makwabta da abokai sukan taru domin cin abinci tare, da yi wa juna fatar alheri da addu'ar Allah Ya karbi ibadarsu.

Irin akidar dake tattare da wannan buki na Sallar Azumi ko Eid-el-Fitr, tana tunatar da mu irin fata, da ingancin halin rayuwar da addinin Musulunci ya haifar ga miliyoyin mutane a kasa ta, da kuma mutane fiye da miliyan dubu daya a fadin duniya. Har ila yau, watan Ramadan, lokaci ne na tuna cewar addinin Musulunci Ya haifar da akida mai daraja ta koyon ilmi wanda ya taimakawa dukkan bil Adama.

A nan Amurka, Musulmi sun bayar da gudumawa a fannonin kasuwanci, kimiyya, shari'a, aikin likita, ilmi da wasu fannonin masu yawa. Musulmin dake cikin rundunar sojojinmu, da wadanda ke cikin gwamnati na, suna aiki mai kyau ga 'yan'uwansu Amurkawa, suna kuma jaddada akidojin kasarmu na 'yanci da adalci a duniyar dake zaune cikin lumana.

Ni da Laura, mai daki na, muna mika sakonmu na fatar alheri ga dukkan Musulmi a nan Amurka da kuma fadin duniya a wannan lokaci na Sallar Azumi. Allah Ya wanzar muku da alhetin watan Ramadan, Ya kuma maimaita mana mu ga na badin-badada.

XS
SM
MD
LG