Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyun Adawa Na Togo Sun Lashi Takobin Yakar Yunkurin Shugaba Gnassingbe Eyadema... - 2002-12-31


Jam'iyyun adawa na kasar Togo, sun lashi takobin yakar wani sabon sauyin da aka yi ga tsarin mulkin kasar, wanda zai bai wa shugaban da ya jima yana mulkin kasar damar ci gaba da mulki na duk wa'adin da ya ga dama.

Shugaban wata tarayyar 'yan adaw amsu neman sauyi da ake kira "Union of Forces for Change", Jean-Pierre Fabre, ya ce watakila zasu nemi jama'a da su yi zanga-zanga. Ya ce tuni har shugabannin jam'iyyun adawa da dama sun gana domin tsara dabarar yadda zasu bullowa lamarin.

Mr. Fabre yayi wannan furucin kwana guda a bayan da majalisar dokokin Togo ta soke ka'idar dake cikin tsarin mulki, cewar shugaba zai yi wa'adi biyu ne kawai na shekaru biyar-biyar a kan mulki. Wannan wa'adi na shugaba Gnassingbe Eyadema zai kare a shekara mai zuwa.

Masu fashin baki suka ce wani gyaran kuma da aka yi ga dokar zabe, an tsara shi ne musamman domin hana shugaban adawa, Gilchrist Olympio, yin takarar shugaban kasa a 2003. Sabuwar dokar ta bukaci mai son tsayawa takarar shugaban kasa da ya zauna cikin kasar Togo na tsawon akalla shekara guda kafin zaben. Shi dai Mr. Olympio yana zaman gudun hijira ne yanzu haka a birnin Paris.

Mr. Eyadema ya hau kujerar shugabancin Togo tun bayan wani juyin mulkin soja da yayi a shekarar 1967, shekaru 35 da suka shige.

XS
SM
MD
LG