Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Bukin Ranar Tuna Martin Luther King A Amurka - 2003-01-20


Amurkawa suna bukukuwan tunawa da rayuwa da kuma ayyukan Martin Luther King Jr., madugun kwatar hakkin bakaken fatar da a yau yake cika shekaru 74 da haihuwa idan da yana da rai.

Yau ranar hutu ce ga ma'aikatan gwamnatin tarayya a duk fadin Amurka domin tuna gwarzon, kuma akasarin ofisoshin gwamnati da cibiyoyin kudi da makarantu suna hutu.

A bayan jagorancin da yayi na gwagwarmayar kwatar hakkin bakaken fatan Amurka, haka kuma Martin Luther King ya mayar da gwagwarmaya cikin ruwan sanyi ba tare da tashin hankali ba, ta zamo amintacciyar hanya ta neman sauyin halin rayuwa a nan Amurka.

A shekarar 1964, an ba shi kyautar lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya. Shekaru hudu bayan wannan, watau a shekarar 1968, wani mutumi ya bindige Martin Luther King Jr. ya kashe shi.

XS
SM
MD
LG