Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NASA Ta Ce Babu Wani Dalilin Kwashe 'Yan Sama Jannati Daga Tashar Bincike A Cikin Sararin Samaniya - 2003-02-03


Jami'an Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Amurka, NASA, sun ce babu wani dalili na kwasshe Amurkawa biyu da dan kasar Rasha guda da suke zagaya duniya cikin tashar binciken kimiyya ta kasa da kasa a cikin sararin Subhana.

Darektan kula da ayyukan 'yan sama jannati na hukumar, Bob Cabana, ya ce 'yan sama janntin dake cikin tashar suna jimami sosai kuma suna fama da kadaici. Amma ya ce suna nuna dauriya, kuma babu wani dalili kwashe su daga cikin tashar.

Mr. Cabana ya bayyana wannan jiya lahadi a Jihar Texas ta nan Amurka, sa'o'i kadan a bayan da Rasha ta cilla wani kumbon da babu mutum a ciki domin yayi dakon kayayyakin masarufin da 'yan sama jannatin dake cikin tashar zasu bukata har zuwa watan Yuni.

Jami'an binciken sararin samaniya na Rasha sun ce ci gaba da aikin gina tashar zai ragu matuka a saboda dakatar da zirga-zirgar jiragen jigila a samaniya na Amurka da aka yi a bayan hadarin jirgin jigilar Columbia.

XS
SM
MD
LG