Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

...Iraqi Ta Bayyana Shaidar Amurka Da Cewa Karya Ce Kawai Tsagwaronta - 2003-02-06


Hukumomin Iraqi sun ce shaidar da sakataren harkokin wajen Amurka, Colin Powell, ya gabatar, karairayi ne kawai da aka kitsa da nufin bai wa Amurka dalili na far ma Iraqi da yaki. Wakilin Muryar Amurka a birnin al-Qahira, Greg Lamotte, ya ce babban jami'in Iraqi dake tare da sufetocin makamai na MDD, Amer al-Saadi, ya mayar da martani ga jawabin na Mr. Powell yana mai bayyana shi a zaman majigi.
ACT: AL SAADI: "This was a typical American show complete with stunts and special effects. What we......"

FASSARA: Wannan tamkar irin majigin nan ne da aka san Amurka wajen iya shiryawa, ciki har da gwaje-gwaje na bagu. Abubuwan da muka ji daga bakin Colin Powell a yau, an tsara sune domin shawo kan jama'ar da ba su san gaskiyar lamarin ba, domin a samu sukunin kai farmaki kan Iraqi. KARSHEN FASSARA

CI GABA: Malam al-Saadi yayi watsi da kaset din da Mr. Powell ya gabatar na muryoyin jami'an sojan Iraqi, yana mai cewa daga ji an san cewa zama aka yi aka kitsa, har ma ya ce kowace hukumar leken asiri ta kasar da ba ta ci gaba ma zata iya hada irin wannan kaset.

Ya musanta zargin da Mr. Powell yayi na cewa masana kimiyyar Iraqi suna boye takardu, ko kuma an boye haramtattun makamai a cikin Iraqi ko kuma a kasashe makwabta.

Ya ce hotunan tauraron dan Adam da Mr. Powell ya gabatar ba su gaskata komai cikin ikirarinsa ba, haka kuma babu gaskiya a cikin bayanan da ya ce wasu bijirarrun 'yan Iraqi ne suka bayar. Malam al-Saadi ya kammala da cewar abin kunya ne ga kasa kamar Amurka ta gabatar da irin wadannan zarge-zarge da ra'ayoyi.

XS
SM
MD
LG