Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Darektan Hukumar Leken Asirin Amurka Yayi Gargadi Game Da Rikice-Rikice A Afirka - 2003-02-12


Darektan hukumar leken asirin Amurka ta CIA yayi kashedin cewa rashin kwanciyar hankali mai muni a kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara zazi bukaci tsoma hannun Amurka.

George Tenet ya bayyana wannan lokacin da yake bada shaida gaban wani kwamitin majalisar dattijai jiya talata, inda ya bayyana hadarurrukandake kunno kai ga Amurka a bayan hare-haren ta'addanci na 11 ga watan satumba.

Mr. Tenet yayi bayani kan rikice-rikicen siyasa da na kabilanci da kuma zarmiya da cin hanci da suka zamo ruwan dare a kasashen Afirka da dama.

Mr. Tenet ya ce rashin karfin tattalin arziki da kuma rikicin addini a Nijeriya suna iya haddasa fitina kafin zabubbukan da za a yi a bana. Ya ce koda yake zai yi wuya duk wata fitina ta shafi danyen man fetur da Amurka take saya daga Nijeriya, dangantaka tsakanin Amurka da Nijeriya tana iya sukurkucewa idan har sojoji suka kwace mulki.

Darektan na hukumar CIA ya kuma ce tana yiwuwa a bukaci taimakon Amurka a sanadin rikicin Zimbabwe.

Mr. Tenet ya tabo yakin basasar kasar Ivory Coast inda ya bayyana a fili cewar kasar tana rushewa a zahiri. Ya ce wargajewar kasar Ivory Coast zata shafi yankin baki daya a saboda raguwar harkokin cinikayyar da zata faru.

XS
SM
MD
LG