Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liberiya Ta Ce Tana Yakar 'Yan Tawaye A Fagagen Daga Hudu - 2003-02-19


Ministan tsaron Liberiya ya ce gwamnbati tana yakar 'yan tawaye a fagagen daga hudu.

Daniel Chea ya ce sojojin gwamnati suna yakar 'yan tawayen Kungiyar L.U.R.D. a Tubmanburg, Gba, Zorzor da Kolahun, mai tazarar kilomita 50 a arewa da Monrovia, babban birnin kasar. Har ila yau ya ce fada ya gusa har zuwa kusa da bakin iyakarsu da kasar Saliyo.

Hukunmar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce ta damu da makomar 'yan Liberiya su dubu 36, wadanda ala tilas suka gudu daga gidajensu a saboda fadan da ake gwabzawa cikin 'yan kwanakin nan.

Ofishin babban jami'in kula da 'yan gudun hijirar majalisar ya ce 'yan Liberiya su kimanin dubu 6 sun gudu suka shiga Saliyo, makwabciyarsu, yayin da wasu dubu 30 suka nemi mafaka a kusa da Monrovia.

Hukumar ta ce tana shirye-shiryen sake tsugunarwa ko kuma mayar da 'yan gudun hijirar Saliyo su fiye da dubu 17 zuwa gida.

XS
SM
MD
LG