Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Girgizar Kasa Ta Kashe Mutane 257 A Kasar China - 2003-02-24


Wata girgizar kasa mai karfin gaske ta jijjiga lardin Xinjiang na arewa maso yammacin China a yau litinin, inda ta kashe mutane fiye da 250, ta raunata wasu fiye da dubu daya.

Karfin wannan girgiza ya kai awu 6 da digo 8 a ma'aunin motsin kasa na Richter.

Girgizar ta jijjiga yankin dake kusa da tsaunukan bakin iyakar China da Kyrgyzstan, kimanin kilomita dubu 2 da 800 a yamma da Beijing, babban birnin kasar. Akasarin mazauna wannan yankin Musulmi ne 'yan kabilar Uighur.

Gidaje da makarantu fiye da dubu daya sun rushe a wani kauyen dake karamar hukumar Bachu, inda wannan girgiza ta fi karfi.

Kamfanin dillancin labaran Xinhua ya ce wannan girgizar kasa ita ce mafi muni da aka taba gani a lardin Xinjiang cikin shekaru 50 da suka shige.

XS
SM
MD
LG